Wata babbar kotun Jihar da ke garin Ilorin babban birnin Jihar Kwara ta yankewa wasu mutane Biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zarginsu da laifin aikata kisan kai da kuma fashin banki a Jihar.

Kotun ta yanke hukuncin ne a zaman da ta gudanar a yau Alhamis.
A yayin yanke hukumar Alkaliyar Kotun Mai shari’a Haleema Saliman ta ce an samu wadanda ake zargin da aikata laifin fashi da makami, kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Alkaliyar ta kara da cewa daga cikin wadanda mutanen suka hallaka ciki har da jam’an tsaron ‘yan sanda da sauran wasu mutane, a yayin harin da suka kai bankin.

Mai shari’ar ta bayyana cewa dukkan wanda aka samu da irin wannan laifin hukuncin kisa ne akanshi.
Ta ce ta kamsu da dukkan hujjojin da masu shigar da kara suka shigar mata, inda suka aka kawo karshen shari’ar.
Mutane Biyar din da ake zargin sun yiwa bankin bankin Offa fashin ne tun a ranar 5 ga watan Afrilun shekarar 2018 da ta gabata, inda aka hallaka mutane 32 ciki har da jami’an ‘yan sanda tara.