Hukumar Yaki da masu yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa ta EFCC ta kai samame dakunan kwanan dalibai na Jami’ar Usman Danfodiyo UDUS da ke Jihar Sokoto, tare da kama wasu daliban jami’ar.

Jami’an hukumar sun kai samamen ne a yau Asabar a unguwannin Kwakwalawa, Gidan Yaro, unguwannin da mafiya yawa daga cikinsu daliban jami’ar ne ke zaune.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun kai samamen ne da misalin karfe 4 na asubahin yau din, tare da kutsawa dakunan daliban suna kama su.

Amma a halin yanzu hukumar ta EFCC ba ta ce komai ba bisa samamen da ta kai ko kuma bayyana dalilin kama daliban.

Ba wannan ne karon farko ba da jami’an hukumar ke kama dalibai kan zargin aikata badakala, inda ko da a bayama sai da jami’an hukumar suka taba kai wani samame Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure a Jihar Ondo FUTA, a watan Fabrairu, tare da balle dakunan kwanan daliban a cikin dare, inda kuma suka kama wasu dalibai biyu da misalin karfe 2 na dare a wajen jami’ar.
A samamen da jami’an suka kai ɗalibai da dama sun dauka masu garkuwa da mutane ne sakamakon yadda suka yi amfani da ƙarfi wajen shiga dakunan daliban.
Rahotanni sun ce jami’an hukumar da suka fito daga ofishin EFCC na yankin Benin, sun kuma lalata kayayyaki tare da cin zarafin ɗaliban ciki har da mata.
Sai dai bayan kai samamen Shugaban hukumar ta EFCC Ola Olukoyede ya dakatar da jami’an daga kai irin wannan samame a cikin dare.