Dubban Al’ummar Jihar Kano da dama ne suka fito a jiya Asabar domin tarar shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdulllahi Umar Ganduje, a yayin wata ziyara da ya kai karamar hukumar Bichi da ke Jihar.

Ganduje ya je karamar hukumar ne domin yin ta’aziyya ga ‘yan uwa da iyalan jami’an ‘yan sandan da suka rasa rayukansu akan hanyarsu ta dawowa Jihar, bayan halartar zaben gwamnan Jihar Edo da aka gudanar a makon da ya gabata.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC ce dai ta tabbatar da mutuwar jami’an ‘yan sanda a ranar Talatar da ta gabata.

Hukumar ta bayyana cewa a yayin hadarin ya rusa da jami’anta biyar, a lokacin da suke dawowa daga Jihar ta Edo bayan kammala zaben gwamnan Jihar a ranar Asabar.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen karfi da ke kan hanyar Zaria zuwa Kano a kusa da filin fakin na manyan motoci.