An sake samun katsewar hasken lantarki a Najeriya karo na biyu cikin awanni 24.

A yau Talata an sake wayar gari da lalacewar tashar wutar kuma shi ne na biyu cikin awanni 24.

Katsewar ta haifar da tsayawar al’amura musamman waɗanda ke da jibi da lantarki.

A wata sanarwa da hukumar rarraba lantarki ta fitar, ta sake bai wa al’umma hakuri dangane da lamarin.

Sannan sun ce su na aiki tukuru don ganin komai ya daidaita.

Kamfaninin rarraba wutar lantarki a jihohin Kaduna, Enugu Abuja da Kano sun bai wa abokan kasuwancinsu hakuri bisa faruwar lamarin.

Lalacewar tashar wutar wannan ita ce karo na bakwai cikin shekarar 2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: