Shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya Malam Mele Kyari ya ce cire tallafin man fetur da aka yi ya taimaka wajen rage fasa kwaurinsa zuwa kasashen makofta .

Kyari ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi dashi da gidan talabiji na Channels.

Ya ce kafin cire tallafin man fetur farashin da ake siyarwa na sanyawa masu fasa kwaurinsa samun gwaggwabar riba.

Sai dai zuwa yanzu an samu karancinsa saboda farashi y kusa da yadda ake siyarwa a kasashen makofta .

Ya ce wannan ci gaba ne kuma nasara ce babba.

A cewarsa cire tallafin ya hana masu fasa kwaurinsa samun ribar da su ke samu a baya.

Kuma hakan ya samu ne bayan da shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cirewa a watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: