Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya amince da siyarwa da dillalan mai na kasar fetur kan naira 995 kowacce lita.

Wannan y biyo bayan shiga tsakani da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi.

Mataimakin shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa Hammed Fashola ne ya sanar da haka wanda ya ce an warware matsaloli da dama da su ke dabaibaye da lamarin.

Fashola ya kuma sake tabbatar da cewar shiga tsakanin ya haifar da sakamakon basu damar siyo mai kai tsaye daga matatar mi ta Dangote.

A sakamakon haka ne ma ya yabawa hukumar tsaro ta DSS da hukumar kula da man fetur ta kasa.

Zuwa yanzu dai kamfanin NNPC zai dinga siyar musu kowacce litar fetur kan naira 995.

Dambarwa a kan man fetur ta sake tsami ne bayan da aka samu karin farashin a makon da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: