Sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi na ll ya nada Alhaji Gambo a matsayin shamakin garin Garko da ke Jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar ya wallafa a shafin X a yau Laraba.

Sanarwar ta tabbatar da cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin Shamakin na Garko ne domin kara inganta masarautar.

Bayan amincewa dashi an kuma gudanar da nadin na shi ne a yammacin yau, a kofar Kwaru da ke gidan Sarkin Sanusi na ll.

Nadin na shi na zuwa ne bayan da Sarkin na 16 Muhammadu Sanusi II ya amince da yin nadin Abba Yusuf, wanda ya kasance kawu ne ga gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin Dan Makwayon Kano, inda kuma za a nada shi a ranar 18 ga watan Oktoban nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: