Gwamnan Jihar Ekiti Biodun Oyebanji ya karrama zakwakuran ma’aikatan Jihar, bisa jajircewar da suke nunawa a yayin ayyukansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da kungiyar ma’aikatan gwamnatin Jihar ta shirya tare da bayar da lambar yabo ta shekarar 2024 a Jihar.
Taron wanda ya gudana a jiya Talata, kuma hakan wani bangare ne na bikin cika shekaru biyu da darewar Biodun kan kujerar gwamnan Jihar.

A yayin taron an karrama ma’aikata 82 ta hanyar ba su lambar yabo da kuma kyautar kudi na Naira miliyan 42 nisa aiki tukuru a bangarori daban-daban na Jihar.

Gwamnan ya bayyanawa ma’ikatan jihar cewa nan ba da jimawa ba za su fara samun sabon mafi karancin albashi.
Sannan gwamnan ya kuma kara jaddada kudurinsa na ma’aikatan jihar sun samu sabon mafi karancin albashi.