Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta dage tantancewar da ta shirya yiwa sabbin ministocin da shugaba Tinubu ya nada ne domin basu damar kammala hada takardunsu.

Hadimin shugaba Tinubu a bangaren Majalisar Sanata Basheer Lado ne ya tabbatar da dagewar a yau Talata.

Sanata Lado ya ce an dage tantance sababbin Ministocin ne zuwa gobe Laraba 30 ga watan Oktoban nan.

Lado ya ce an dauki matakin ne domin ba sababbin Ministocin damar kammala shirye-shiryensu kafin tantancewar da za a yi musu a goben da misalin karfe 12:00 rana.

A yau din ne dai Majalisar Dattawa ta Kasa za shirya tantance sabbin ministocin da shugaban ya nada amma daga bisa kuma aka dage ranar tantancewar.

Nada sabbin ministocin na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa, inda ya dakatar da Ministoci biyar daga bakin Aiki.

Inda kuma bayan dakatarwar da shugaban yayiwa Ministocin, daga bisa kuma ya nada wasu bakwai, ya yin da ya hade wasu ma’aikatu tare da rushe wasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: