Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi tir da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sakamakon abin da ya kira zalunci bisa gurfanar da ƙananan yara a gaban kotu domin yi musu shari’a.

Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wallafa da yayi a shafinsa na X a jiya Juma’a, ya ce ya damu da bidiyon yaran da aka nuna bayan yunwa ta yi musu illa tun bayan tsare su da aka yi.
Atiku ya ce abin abin tayar da hankali ne da kuma takaici, tare da bayyana yadda gwamnati ke nuna rashin kulawa da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ƙananan yara.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan ya bai’wa ƙananan yara cikakken ’yancin da mutuntawa, amma abin mamakin sai suka rasa hakan a cikin Kasar su Najeriya.

Acewar Atiku ƙananan yara wadanda su ne suka fi shan wahala akan manufofin gwamnatin Bola Tinubu, su na da damar gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama.
