Gwamnatin tarayya ta yi karin bayani akan daina turawa Jihar Rivers Kudaden wata-wata daga Tarayya.

Daraktan yada labaran ofishin akanta Janar na Tarayya Mista Bawa Mokwa ne ya bayyana hakan a yau Asabar ga Jaridar Tribune.
Bawa ya bayyana cewa har yanzu ta na aikewa da Jihar ta Rivers kudaden bisa wani rahoto da ke nuni cewa an daina bai’wa Jihar ta Rivers kudaden wata-wata.

Daraktan ya kara da cewa har kawo yanzu gwamnatin na ci gaba da aikewa da kudaden watan Oktoba wanda asusun gwamnatin tarayya ke bai’wa Jihohin Kasar nan da kananan hukumomi.

Acewar Bawa Jihar Rivers itama za ta samu nata rabon sakamakon karar da aka yi kan hukuncin kotu da ya bai’wa Jihar ta Rivers kudaden wata-watan.