Hadakar ‘yan takarar Gwamna a Jihar Ondo na jam’iyyun Siyasa daban-daban na Jihar sun nuna goyan bayansu ga nasarar gwamnan Jihar Lucky Aiyedatiwa.

Hadakar ‘yan takarar na jam’iyyun NNPP, APGA, LP, APM, AA, APP, ADP, ADC, YP, YPP, BP, da kuma ZLP, ne suka bayyana hakan a jiya Juma’a a yayin wata ganawa da suka yi da Aiyedatiwa da shugabanin jam’iyyunsu a dakin taro na gidan gwamnatin Jihar.

A yayin taron ‘yan takarar sun sun bayyana amincewarsu da nasarar Aiyedatiwa, tare da bayyana kudurinsu na hada kai don yin aiki tare domin ganin sun gina sabuwar Jihar ta su.

‘Yan takarar jam’iyyun sun kuma bukaci da Aiyedatiwa da ya tafi da sauran jam’iyyun siyasa na Jihar da suka yi takara da shi.

A jawabin gwamnan Lucky ya nuna jindadinsa bisa goyan bayansa da abokan takarar tasa suka yi da shugabannin jam’iyyun, inda kuma ya bayyana cewa zai tabbatar da ganin ya hada kai da su da masu ruwa da tsaki na Jihar domin ciyar da jihar gaba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: