An yi kira ga ma’aikatan hukumar samar da wutar lantarki a karkara da su bai’wa sabuwar babbar sakatariyar mulki ta ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma ta Jihar kano goyon baya domin ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.

Daraktan hukumar samar da wutar lantarki a karkara Injiniya Sani Bala ne ya bayyana hakan a yayin da yake karbar babbar sakatariyar a ofishinsa,tare da tabbatar da goyon bayansa gareta da kuma ma’aikatansa.
Daraktan ya kuma godewa gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa zabar Hajiya Fatima Adamu a matsayin babbar sakatariyar ma’aikatar raya karkara.

A yayin jawabinta a ziyarar Hajiya Fatima Adamu ta godewa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa nada ta da yayi a matsayin babbar sakatariyar.

Ta kuma sha alwashin yin aiki da gaskiya, tare da tabbatarwa da ma’aikatan raya karkara da cigaban al’ummah dama sauran ma’aikatan sassa da ke karkashin ma’aikatar goyon baya wajen gudanar da ayyukansu.