Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya duk da cewa wasu na yi masa fatan mutuwa.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a garin Osogbo na Jihar Osun, a lokacin da yake bude titin Old-Garage/Oke-Fia, wanda Gwamna Ademola Adeleke ya kara ginawa a Jihar.
Olusegun Obasanjo na wannan kalaman ne bayan bullar wata jita-jita a kafafan sada zumunta cewa ya mutu.

Acewar tsohon shugaban na Najeriya, bayan ganin da yayi a shafukan sada zumunta cewa ya mutu, ya gaggauta sanar da ’ya’yasa da ‘yan uwansa cewa ba gaskiya ba ne abinda ake yadawa,inda ya ce yana nan da raansa.

Obasanjo ya kara da cewa mutanen da ke yi masa fatan ya mutu, burinsu kenan, amma Allah ya kareshi.
A yayin bude titin Obasanjo ya jinjinawa gwamna Ademola, sakamakon nasarorin da ya samu a jihar ta Osun, inda ya shawarci gwamnan da ya ci gaba da gudanar da kyawawan ayyuka a fadin Jihar.
A yayin gwamna Adeleke ya shaidawa al’ummar Jihar cewa gwamnatinsa za ta kammala dukkanin ayyukan da ake yi a Jihar.
Gwamna Ademola ya ce yana matukar alfahari da gina hanyoyi fiye da kilomita 120 a fadin jihar, inda ya bayyana cewa akwai gadoji biyu masu girma da ake dab da kammalawa a Osogbo, inda ake ci gaba da aiki a gadar Ile-Ife da kuma hanyar da aka ninka zuwa biyu a Ilesa.
Har ila yau gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne akan kammala hanyar Iwo-Osogbo. Sannan ya ce sun kara aikin gina hanyar Odoori-Adeeke a Iwo, wanda za a yi ta a matakai biyu.
Acewarsa Matakin farko zai fara daga Post Office zuwa Fadar Oluwo, mataki na biyu kuma zai tashi daga Post Office zuwa mahaɗar Adeeke.
Gwamna Ademola Adeleke ya kuma tabbatar da cewa ba za su karbo bashi ba domin kammala ayyukan ba, sakamakon datse hanyoyin zurarewar kudin gwamnatin Jihar, inda suka yi amfani da albarkatun cikin gida domin rage kudin ayyukan.