Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta bai’wa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon Kasa EFCC umarnin tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Alkaliyar kotun Mai shari’a Maryanne Aninih ce ta bai’wa hukumar ta EFCC umarnin tsare Yahya Bello a hannunta, tare da sanya ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan bukatar bayar da belinsa.

Lauyoyi daga bangarorin hukumar ta EFCC da na Yahya Bello sun tafka muhawara kan buƙatar bayar da belinsa.

Lauyan Yahya Bello Joseph Daudu SAN ya roki da kotun ta bayar da belinsa, tare da ya bayyana cewa laifuffukan da ake zargin Yahya Bello da su na daga cikin wadanda za a bayar da belinsa.

Amma lauya mai gabatar da kara Kemi Pinheiro SAN ya kalubalanci buƙatar belin.

Yahya Bello da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Jihar ta Kogi Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, an zarge su da baki wajen yin amfani da kudaden gwamnati domin sayen kadarori a Abuja da Kasar Dubai na akalla Naira biliyan 110.4.

Kafin fara zaman kotun sai da aka sanya tsaro a wajen kotun, inda jami’an sojoji, DSS, EFCC, da ‘yan sanda suka mamaye kotun.

Hukumar ta EFCC ta dai gurfanar da Yahya Bello a gaban kotun ne a yau Laraba, bayan mika kansa da yayi gareta a jiya Talata, bayan shafe tsawon lokaci da ta yi tana nemansa sakamakon kin amsa gayyatarta da yayi bisa zargin da take yi masa na aikata almundaha a lokacin da yana kan kujerar gwamnan Jihar ta Kogi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: