Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun shiga garin Keke A da ke Millennium City da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da wani yaro mai shekaru biyu tare da wasu ‘yan uwansa mata uku.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9;00 na daren jiya Talata, bayan da mahaifin yaran ya je duba mahaifiyarsu a asibiti, bayan kwantar da tagwayen da ta haifa a kwanakin baya asibitin.

Daga cikin wadanda yaran da maharan suka yi garkuwa da su akwai yaro mai shekaru 2, da mai shekaru 9 , da shekaru 12 da kuma shekaru 15.

Mahaifin yaran mai suna Yunusa Sarkin Samarin Keke, ya ce daya daga cikin yaran maraya ne da yake kula da shi.

Yunusa ya bayyana cewa bayan dawowarsa daga Asibitin ya tarar maharan sun dauke dukkanin yaran, amma wani kanin yaran da ke bacci maharan ba su tafi da shi sakamakon lullbe jikinsa da yayi.

Mahaifin yaran ya kara da cewa yana zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa yaran, bisa cewa an samu takalman yaran a watse a kofar gida, kuma gidansa kadai aka kai wa harin.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa Yankunan Keke da Millennium City da ke Jihar ta Kaduna na ci gaba da fuskantar ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Mansur Hassan kan lamarin ba a samu ji daga bakinsa sa ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: