Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta sanya ranar Juma’a mai zuwa 29 ga watan Nuwamba nan a matsayin ranar ga ma’aikatan Jihar.

Gwamnatin Jihar ta bayar da hutun ne domin girmama uwargidan gwamnan Jihar Umo Eno, wato marigayiya Fasto Patience Umo Eno.

Sakataren gwamnatin jihar Prince Enobong Uwah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Laraba.

Sakataren ya ce gwamnatin Jihar ta bayar da hutun ne bisa shirye-shiryen da ake gudanarwa na kai marigayiyar zuwa makwancinta, bayan tuntubar iyalan marigayiyar kan bayar da hutun.

Sakataren ya kara da cewa an dauki matakin hakan ne domin bai’wa ‘yan Jihar damar yin bankwana da marigayiyar, inda za a ajiye ta a ranar a Ikot Ekpene Udo Karamar hukumar Nsit Ubium ta Jihar.

Idab a manta ba a ranar 26 ga watan Satumban shekarar nan gwamnatin Jihar ta Akwa-Ibom ta tabbatar da mutuwar uwargidan gwamnan, bayan gajeriyar jinya a wani asibiti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: