Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tabbatar da cewa akwai alaka mai karfi tsakanin Najeriya da Kasar Faransa.

Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafin X a yau Juma’a.
Acewar Bayo, Shugaban Tinubu ya bayyana cewa yana da yakin cewa alakar Najeriya da Faransa za ta amfanar da Nahiyar baki daya.

Sunday Dare hadimin shugaban kan yada labarai, shima a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X, ya ce shugaban Kasa Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da na Faransa da su ci gaba da kulla alaka tsakaninsu.

Shugaban na wannan kiran ne ga ‘yan kasashen biyu a wata liyar cin abincin dare da shugaban Kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya shirya musu a jiya Alhamis.
Shugaba Tinubu ya kara da cewa kafin Kasar Faransa ta hau kan matakin da ke a yanzu ta sha gwagwarmaya, har ta kai ga ta tsaya da kafafunta, inda kuma hakan ya zama abin koyi ga Najeriya.