Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar korar ‘yan sabuwar kungiyar Lakurawa da dama daga Kasar.

Mukaddashin babban kwamandan runduna ta Takwas ta sojin Najeriya da ke Jihar Sokoto Birgediya Janar Ibikunle Ajose ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a Jihar Sokoto a yayin zantawa da manema labarai, a madadin Babban kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma Manjo Janar Oluyinka Soyele.

Oluyinka ya ce jami’an sun kuma lalata sansanoni akalla 22 na ƴan ta’addan a jihohin Sokoto da Kebbi.

Acewar Oluyinka babban hafsan hafsoshin tsaro Kasar nan Janar Christopher Musa ne tuni ya aike da rundunar ta musamman domin gudanar da aikin fatattakar ‘yan ta’adda daga Kasar.

Kazalika ya ce jami’an sun samu nasarorin ne ta hanyar kai hare-hare kan ‘yan kungiyar ta Lakurawa tare kuma da lalata sansanoninsu.

Sannan ya umarci sojin da su tabbatar da korar ‘yan ƙungiyar ta Lakurawa, tare da bukatarsu da su bu dukkan dokokin aiki da kuma tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: