Jam’iyyar PDP ta Kasa ta musanta batun da ke yawo cewa tana neman hadin kan tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan, don yi mata takarar shugaban Kasa, a kakar zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Kakakin jam’iyyar na Kasa Ibrahim Abdullahi ne ya musanta rahotan, yana mai cewa ko kadan babu gaskiya a cikin rahotan da ake yadawa.
Kakakin ya ce ko kadan babu wani lokaci da jam’iyyar ta PDP ta nemi da Jonathan da ya yi mata takara ko kuma ta bukaci da ya fito yayi takara a zaben 2027.

PDP ta ce kawai mutane na yada kanzan kurege ne kawai akan hakan amma jam’iyyar ba ta san da wannaan batun ba.

Jam’iyyar ta kara da cewa Janathan yana da damar tsayawa takara matukar yana da bukatar hakan duba da kasancewarsa dan Kasa, amma ta ce ko kadan tsohon shugaban bai nuna sha’awar tsayawa takara ba, ballanta na jam’iyyar ta tuntube shi.
Ibrahim Abdullahi ya ce PDP tana da ’yan takarar da suka cancanta daga cikin gwamnoni da kuma shugabanni da dama a yanzu.
Acewar Kakakin jam’iyyar ba za ta dogara ga wanda bai nuna sha’awar tsayawa takara a cikinta ba.