Gwamnan Jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya sauyawa wasu daga cikin kwamishinoninsa Ma’aikatu don kara inganta ayyukan gwamnatin Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar.

Sanarwar ta ce a sauyawa kwamishinonin Ma’aikatu da gwamnan yayi, ya nada Alhaji Malik Anas a matsayin sabon kwamishinan Ma’aikatar Tsare-Tsare da Tattalin Arziƙi, wanda a baya ya taba rike mukamin Akanta-Janar na Jihar ta Katsina, yayin da kuma mamba ne a kungiyoyin kwararru daban-daban.

Sannan gwamnan ya mayar da Alhaji Husaini Kagara Ma’aikatar kudi ta Jihar, wanda shima a baya shine Kwamishinan Ma’aikatar tsare-tsare da Tattalin arziki na Jihar.

Har ila yau gwamna Radda ya aike da Bashir Tanimu Gambo Ma’aikatar harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, wanda tsohon kwamishinan kudi ne.

Sauran sun hada da Alhaji Yusuf Rabi’u Jirdede Ma’aikatar Kasuwanci, Ciniki da Zuba Jari, inda a baya yake Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, sai kuma Alhaji Adnan Nahabu da ke Ma’aikatar Kasuwanci Ciniki da Zuba Jari, inda gwamnan ya mayar dashi Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: