Shugaban karamar hukumar Soba a jihar Kaduna Hon Muhammad Lawal Shehu ya amince da karawa Limaman Masallatan Juma’a na Karamar hukumar alawus-alawus din da ake ba su kowanne wata.

Shugaban Karamar hukumar ta Soba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani taron limaman Masallatan Juma’a a Sakateriyar Dahiru Maigana, inda ya ce ya dauki matakin hakan ne, bayan hawanshi ta tarar an datakar da bai’wa Limaman alawus din da ake basu kowanne wata.

Shehu ya kara da cewa bayan ganowar da yayi an dakatar da bai’wa Limaman alawus, ne ya bayar da umarnin yin nazari akan alawus din da ake biyansu a baya, daga bisani kuma a yi musu akan na bayan, sakamakon halin kunci da ake fuskanta.

Shugaban Karamar hukumar ya kara da cewa Limaman Masallatan Juma’a na matukar bayar da gudummawa wajen yada manufofin gwamnati ga al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar ta Soba, inda ya ce ya zama wajibi a kara karfafa musu gwiwa.

Acewarsa bayan dakatar da alawus din Limaman a baya, a halin yanzu an dawo da biyan Limaman kudaden watannin biyu da suka gabata, sakamakon cewa a bayan ana biyansu abinda bai taka kara ya karya ba, inda ya ce ya bayar da umarnin fara yi musu kari daga wata mai kamawa.

Sanna shugaan Karamar hukumar ya kuma yi kira a garesu da su yi amfani da karatuttukan da suke yi wajen fadakar da matasa illar shaye-shayen kwayoyi, daba da sauran laifuka marasa kyau don ganin karamar hukumar ta ci gaba.

A yayin jawabinsa a madadin sauran Limaman babban limamin Masallacin Juma’a na Sakaru Malam Ibrahim Aliyu Bagaldi, ya jinjinawa shugaban Kasamar hukumar bisa namijin kokarin da yake yi na sanya Limaman a cikin harkokinsa.

Ya kara da cewa Malaman addinin musulunci a karamar hukumar za su yi amfani da matsayinsu wajen yin fadakarwa da kuma addu’ar samun zaman lafiya da kuma cigaba a karamar hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: