Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume ya jajantawa rundunar Operation Hadin Kai da ke garin Maiduguri bisa rasa jami’anta Shida da ta yi.

Sanatan ya jajantawa sojin ne a lokacin da ya kaiwa Rundunar wata ziyara a jiya Talata.
Sannan Ndume ya kuma jajantawa ‘yan uwa da iyalan Jami’an da suka rasa rayukansu a harin da mayakan ISWAP suka kai a Sabon Gari da ke karamar hukumar Damboa a Jihar.

Acewar Ndume ba za su gajiya ba wajen ci gaba da bai’wa rundunar gudummawa don ganin ta ci gaba da samu nasara a yaki da ‘yan ta’adda da ta ke yi a Kasar.

Ndume ya kuma bukaci al’umma da kada su gajiya wajen marawa jami’an sojin baya a mayaki da ‘yan ta’adda da suke yi a yankin.
Sannan Sanata Ali Ndume ya jinjinawa jami’an bisa kokarin da suke yi na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.
Ya kuma yi addu’ar neman samun sauki ga wadanda suka jikkata a yayin harin, tare da karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.