Hukumar Kashe Gobara ta Kasa ta bayyana irin nasarorin da ta samu a shekarar 2024 da ta gabata.

Hukumar ta ce a shekarar da ta gabata ta 2024, an samu a sarar dukiya da ta kai ta Naira Biliyan 67.1, tare da rasa rayukan mutane 100 bayan tashin gobara daban-daban da aka samu a Kasar.
A yayin ganawa da manema labari a birnin tarayya Abuja a yau Juma’a Shugaban Hukumar na Kasa Abdulganiyu Jaji, ya ce Hukumar ta su ta samu nasarar ceto rayuka mutane 30,890 da kadarorin da kimarsu ta kai Naira Tiriliyan 1.94 bayan tashin gobarar a sassa daban-daban na Kasar nan.

Jaji ya ce mafiya yawan abinda ke hadda gobara shi ne rashin bin dokoki da kuma sakaci, inda ya gargadi mutane da su kula matuka domin domin gujewa tashin gobara.

Sannan jaji ya kuma jajantawa ‘yan uwa da iyalan da wadanda suka rasa rayukansu a yayin tashe-tashen gobarar.