Kasar Amurka ta dawowa da Najeriya dala miliyan 52.88 daga dukiyoyin Galactica da aka boye a Kasar.

Kasar ta Amurka ta dawowa da Najeriya kudin ne bayan ta kwato daga tsohuwar Ministar man fetur ta Najeriya Diezani Alison Madueke.

Jakadan Kasar ta Amurka a Najeriya Mr. Richard M. Mills, Jr ne ya jagoranci mayar da kudin zuwa ofishin Ministan shari’a na Najeriya Lateef Fagbemi SAN a yau Juma’a a Abuja.

A yayin mika kudin Jakadan na Amurka ya bayyana cewa tsohuwar Ministar tare da wasu mutane, sun sayi wasu rukunin gidaje na alfarma a biranin California da New York, da sauran wasu abubuwan.

A jawabin ministan a madadin gwamnatin tarayya Lateef Fagbemi ya bayyana cewa dawowa da Najeriya kudaden wani babban mataki ne na himmar da gwamnatin Najeriya ke da ita na yaki da cin hanci da rashawa.

Acewar Fagbemi za a yi amfani da dala miliyan 50 gurin samar da hasken wutar a karkara ta hanyar hadin gwuiwa da Bankin Duniya.

Ya kuma ce ragowar dala miliyan 2.88 kuma za a bai’wa Cibiyar Shari’a ta Duniya domin kara buda tsarin shari’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: