Rundunar yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar jami’an ta biyu yayin da mayakan Boko Haram su ka kai musu hari.

Mayakan sun kai hari ofishin yan sandan da ke Gajiram a ƙaramar hukumar Ngamzai jiya Alhamis
Mai magna ada yawun yan sanda a jihar Kenneth Daso ya tabbata da lamarin wanda ya ce baya ga jami’an su biyu da aka kashe akwai guda da ya samu rauni.

Sai dai sun dakile yunkurin mayakan na kokarin farwa ofishin yan sandan

A cewarsa an yi musayar wuta da jami’an wanda ya sa su ka tsere tare da barin makamansu.
Kwamishinan yan snada a jihar ya yabawa jami’an sa tate da muka sakon taaziyyarsa ga iyalan wadanda su ka mutu.