Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta yi kira da a fitar mata da naira biliyan 126 a matsayin kudaden da za ta yi amfani da su a shekarar nan ta 2025 da muka shiga.

Shugaban hukumar na Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya je gaban kwamitin Majalisar dokokin Kasar domin kare kasafin kudin hukumar a jiya Juma’a.

Farfesa Yakubu ya bayyanawa Kwamitin cewa Hukumar za ta yi amfani da kudaden ne wajen yin cigaba da aikin rajistar zaɓe, tare da shirya zabukan wasu jihohin a wannan shekarar da kuma canja wasu kayyakin aikin zaben da suka samu matsala, sai gyaran ofisoshin hukumar da ke wasu Kanann hukumomi.

Sannan ya ce wannan shekarar ta 2025, shekara ce mai matukan amfani ga hukumar duba cewa za ta shirya zabukan shekarar 2027 mai zuwa.

Shugaban ya kara da cewa zabe a Najeriya ana bukatar isassun kudi, wanda hakan ya sanya hukumar ta nemi naira biliyan 126 don gudanar da komai yadda ya kamata.

Shugaban ya kuma ce hukumar na da takardun da ke dauke da bayanan yadda za ta kashe kudade da ake buƙata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: