Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima ya jagoranci shugabannin majalisa da shugabanin tsaro zuwa taron tunawa da yan mazan jiya.

An gudanar da taron ne yau Laraba a Abuna domin tunawa da jami’an soji da su ka rasa rayukansu a bakin daga.
Haka kuma a karfafawa waɗanda su ke a rage gwiwa wajen ci gaba da aikin tsaron ƙasar.

Daga cikin waɗanda su ka halarta akwai shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio da shugaban majalisar wakilai Tajudden Abbas ai mataimakinsa Benjamin Kalu da babbar alƙaliyar Najeriya Justice Kudirat Kekere Ekun.

Haka kuma akwai ministan Abuja, da shugaban sojin sama da na ƙasa da sojin ruwa da babban sufeton yan sanda na ƙasa.
Sannan akwai karamin ministan tsaro Bello Matawalle da babban hafson tsaron ƙasa Janar Christopher Musa.
A yayin taron an gudanar da al’adu da aka saba don girmama yan mazan jiya.
A 15 ga watan Janairun kowacce shekara ake bikin tunawa da ƴan mazan jiya wanda ake yi a duk faɗin duniya.