Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga watan nan na Janairu 2025 za ta fara turawa Kananan hukumomin Kasar kudade kai Tsaye.

Hadimin shugaba Tinubu na musamman kan yada labarai Sunday Dare ne ya tabbatar da hakan a jiya a wata tattauwa da tashar Arise.
Dare ya ce gwamnatin tarayya za ta fara turawa kananan hukumomin kudaden kai tsaye ne don, domin cika umarnin Kotun Koli da ta bai’wa kananan hukumomin cin ‘yancin gashin kansu.

Sunday Dare yace duk da cewa gwamnatin tarayyar na fuskatar suka akan hakan, amma hakan ba zai hana ta aiwatar da tsarin biyan kananan hukumomin ba kai tsaye.

Sannan Dare ya yi kira ga al’ummar Kasar da su sanya idanu akan yadda Jihohinsu da Kananan hukumominsu ke kashe kudaden da suke samu daga tarayya.
Gwamnatin ta tarayya ta dauki matakin fara biyan kananan hukumomin kaitsaye ne bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke tun a watan Yulin 2024, kai bai’wa kananan hukumomin cin ‘yancin gashin kansu.