Kwamishinan Kananan Hukumomi da masarautu na Kano Alhaji Tajo Othman ya ce ya mayarwa da gwamnatin kano rarar naira miliyan 100 sakamakon yawan da kudin suka yi, wajen sayan kayan makaranta ga makarantun firamare wanda gwamna Abba ya rabawa daliban makarantun a kananan hukumomin Jihar 44.

A hirar sa da manema labarai a jiya Juma’a Kwamishinan, ya ce yayi hakan ne bisa koyi da yayi da shugabanci nagari irin na gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya kasance abin koyi.
Kwamishinan ya ce ayyukan gwamnan Abba Kabir Yusuf sun zamar masa darasi harma da sauran shugabanin wajen yin riko da gaskiya da amana, da kuma kishin Jihar.

Alhaji Tajo ya kara da cewa bai taba tunanin cewa gwamna Abba zai shelantawa al’umma cewa ya mayar da sauran kudin zuwa ga asusun gwamntin Jihar ba, inda kuma gwamnan ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon kayan makarantar don karfafa gwiwar matasa da sauran al’umma don hakan ya zama abin koyi garesu na rikon gaskiya da amana a dukkan lamuransu.

Har ila yau Kwamishinan ya ce a matsayinsa na shugaban Kwamitin dinka kayan makaratun Firemare na Jihar da gwamnan zai raba kyauta, gwamnan Abba ya bashi amanar aikin da kuma bukatar yin adalci da gaskiya a yayin aikin.
Gwamna Abba dai ya ware naira biliyan biyu don samar da kayan makaranta kyauta ga yara na makarantun firamare 798,000 na Jihar, inda kuma bayan kammala aikin Kwamishinan ya mayar da sauran kudaden aikin.