Hukumar rarraba hasken wutar lantarki ta Kasa ta bayyana cewa wasu batagari sun sace tare da lalata layin da ke samar da wutar lantarki a wasu daga cikin sassan birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Juma’a, mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta Ndidi Mbah.

TCN ta bayyana cewa batagrin sun yi barnar ne a layin wuta na 132kv, tare da wayoyin da ke karkashin kasa, da ke kai wutar cikin birnin na Abuja da kuma wasu unguwannin da ke kewaye da ita.

Sanarwar ta kara da cewa layin wutar shine ke bai’wa hukumar rarraba hasken lantarkin na Kamfanin AEDC, da ke samarwa da al’umma wutar.

Acewar sanarwa lamarin ya shafi sama da kaso 60 cikin 100 na wutar da ake samarwa a birnin na Abuja, inda ta ce a halin yanzu jami’an na aiki tukuri don ganin sun gyara wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: