Gwamnatin Jihar Neja ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa ta bude wani shafi da mutane ka iya shiga su yi rijista don samun tallafi ga matasa da manoma a Jihar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar Abubakar Usman ya fitar a yau Talata.

Sanarwar ta gargadi mutane akan shiga shafin wanda ‘yan damfara suka bude shi, kuma sun yi hakan ne don dakile domin batawa gwamnatin Jihar suna.

Acewar sanarwa gwamnatin Jihar ba ta kaddamar da wani shafi ba ko wani abu da ya danganci haka, ya ce dukkan wani abu da gwamnatin za ta gudanar za ta sanar ne ta shafukanta a hukumance ko kuma shafukan sada zumunta da ta amince da su.

Sanarwar ta bukaci al’umma da su kaucewa bayar da bayanansu a irin wadandan shafuka na ‘yan damfara, da ke amfani da sunan gwamnati wajen zaluntar mutane ta hanyar karbar bayanansu na bogi.

A karshe sanarwar ta yi kira ga mutane da su dunga bayar da bayanai fa dukkan wani abu makamancin haka ga hukumomin tsaro don daukar mataki akai.

anta

Leave a Reply

%d bloggers like this: