Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta ƙaddamar da yin bitar mako-mako ta shekarar 2025 a cibiyoyi guda tara.

Wannan yana ƙunshe cikin wata sanarwa wacce jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Sulaiman Dederi ya fitar yau Talata a Kano.

Dederi ya ruwaito babban shugaban hukumar Lamin Danbappa na faɗin hakan a wata ganawarsa da Malaman Addini, waɗanda za su jagoranci bayar da bitar a kowacce cibiya da ke faɗin jihar.

Shugaban hukumar wanda daraktan gudanar da mulki da ayyuka na hukumar Yusuf Mukhtar ya wakilta ya bayyana cewa, cibiyoyin bayar da bitar sun haɗar da Bichi, Doguwa, Gwarzo, makarantar koyar da Ilimin Larabci ta SAS, Rimin Gado, Gezawa, Kura, Rano da kuma Wudil.

Danbappa ya buƙaci yin addu’a daga wurin malaman da ke faɗin jihar, don gabatar ayyukan aikin hajjin shekarar 2025 cikin nasara.

Ya kuma buƙaci maniyyata aikin na hajji da su dinga halartar wurin ɗaukar bitar a cibiyoyinsu, don samun Ilimin yin ibadar ta hajji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: