
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya bayyana cewa rikakken dan bindiga Bello Turji na son mika wuya ga jami’an tsaro bayan ruwan wuta da sojoji suka tsananta kai’wa maboyarsa.
A hirarsa da Channels TV a jiya Juma’a Janar Musa ya ce tun bayan hallaka mataimakin Bello Turji da wasu manyan kwamandojin soji suka yi, Turji ya fara kokarin mika wuya ga Jami’an.

Janar Musa ya kara da cewa tun bayan hallaka mataimakinsa da wasu yaransa, hakan ya sanya ya saki mutanen da yayi garkuwa da su, inda kuma ya bayyana aniyarsa ta mika wuya ga jami’an tsaron Kasar.
