Wasu yan bindiga sun bukaci a biya Naira miliyan 540 don fansar wani ma’aikacin jinya, da kuma wasu mutane da su ka yi garkuwa da su a wani asibiti da ke jihar Katsina.

Tun a baya dai, yan bindigar sun kai hari a kwana-kwanan nan zuwa babban asibiti a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda su ka harbi wani likita da kuma wani ma’aikacin lafiya a asibin, ya yin da su ka yi awon gaba da malamin jinya da kuma wasu mutanen.

Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su wato Yusuf Muhammad Mairuwa, shi ne mataimakin daraktan ayyukan jinya, kuma shugaban sashin aikin jinya na asibitin.

Yan bindigar dai sun bukaci a biya Naira miliyan 270 don sakin jami’in jinyar, sai kuma Naira miliyan 270 don fansar sauran m’aikatan asibitin, da kuma wasu ma’aikatan kamfanin sarrafa takin zamani da su ma aka yi garkuwa da su yayin kai harin.

Gwamnan jihar ta Katsina Dikko Umaru Radda tuni ya nuna damuwarsa da faruwar harin, inda ya jadda cewar gwamnati za ta yi iya kokarinta don tsare rayukan ma’aikatan lafiya a jihar, kuma an bayyana cewa, tuni gwamnati ta dukufa don ganin an kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su ba tare da sun cutu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: