Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane Biyar a lokacin da suka kai hari Kauyen Akansan-Garmadi da ke yankin Rumaya a cikin karamar hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Sannan ‘yan bindigar sun kuma hallaka wani matashi 27 Piti Ezekiel a wani sabon hari da suka kai a Kauyen.
Sakataren kungiyar ci gaban karamar hukumar Kauru Danbaba Katuka ne ya tabbatar da hakan a jiya Juma’a a yayin tattaunawa da jaridar Punch ta waya.
Katuka ya bayyana cewa ƴan bindigan sun harbi wani mutum mai riƙe da mukamin sarautar gargajiya a masarautar Kumana mai suna Timothy Daure mai shekaru 48.

Ya ce ƴan bindigan sun kai hari ƙauyen ne a ranar Alhamis da misalin karfe 10:30 na dare, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Sakataren ya kara da cewa sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a yankin hakan ya tilastawa mazauna yankin tserewa daga yankin domin tsira da rayuwarsu.
Sannan ya ce manoma ma a yankin sun kauracewa zuwa gonakinsu, don kaucewa harin ‘yan bindigar.
Har kawo wannan lokaci ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Mansur Hassan Ba.