Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa, idan hukumomin tsaro sun haɗa ƙarfi za su iya magance matsalar tsaron da ta addabi arewacin Najeriya.

A tattaunawarsa da wata kafar yaɗa labarai Gumi ya yi magana sosai akan shirin sasancin zaman lafiya da ya wakana kwanan nan, tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kuma ƴan tayar da kayar baya, inda ya bayyana cewa hakan ya samar da zaman lafiya a jihar.
Malamin ya kuma jinjinawa shirin bisa wanzuwarsa, inda ya ce sun ga yadda rashin tsaron ya ke lalata tattalin arzikin arewacin Najeriya, amman sakamakon yarjejeniyar yanzu an samu zaman lafiya.

Sai dai Gumi ya bayyana jami’an tsaron a Najeriya ba sa yin aikin cikin haɗaka, kuma ba su da ra’ayin yin sulhu da ƴan ta’addar, wasu ma su na ganin hakan kamar wata gazawa ce.

A ƙarshe ya bayyana cewa tsarin da sabuwar gwamnatin ta zo da shi ya na haifar Ɗa mai ido, don tuni an bude kasuwar Birnin Gwari, tituna su na zaune ƙalau cikin zaman lafiya.