Sanata Adams Oshimole mai wakiltar jihar Edo ta Arewa ya zargin cewa, tsofaffin jami’an tsaro ne su ke yin aikin haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a faɗin ƙasar nan.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasar ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin da shugaban kwamitin albarkatun ƙasa na majalisar dattijai Ekong Samson ya miƙa rahoton kare kasafin kuɗin kwamitinsa a gaban majalisar.
Oshimole ya bayyana cewa tsofaffin janar-janar ɗin soje ne su ke aikata aikin haƙar ma’adanan ba bisa ka’ida ba, kuma sun san su gaba ɗaya.

Ya kuma kara da cewa lokacin da ya na shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya rubutawa tsohon shugaban (Kasa Muhammadu Buhai takarda tare da sanar da shi akan batun.

Ya kuma bayyana yadda tawagar da ya jagoranta don aiwatar da zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar Zamfara sun fuskanci tsananin ƙalubalen tsaro, sakamakon yawan masu aikin haƙar ma’adanan ba bisa ka’ida ba.