Majalisar dokokin jihar kano ta amince da fadada titin zuwa Katsina da yin gada daga gadar kofar ruwa zuwa rijiyar lemo a Jihar.

Majalisar ta amince da kudurin ne, bayan gabatar da kudirin hadin gwiwa kan fadada titin da yin gadar wanda Alhaji Lawan Hussaini Chediyar yan-gurasa mai wkiltar karamar hukumar Dala, da Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo na Karamar hukumar Ungogo, da kuma Alhaji Tukur Muhammad mai wakiltar karamar hukumar Fagge suka gabatar da kudurin a gaban Majalisar.
A yayin gabatar da kudurin dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Dala Alhaji Lawan Hussaini ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar.

Alhaji Husaini ya kuma bayyana muhimmancin titin ga al’umma da kuma irin cunkoson da titin Ke haifarwa.
Alhaji Tukur Muhammad Fagge, da Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo suma sun kara jaddada goyan bayansu akan kudurin.

A wani ci gaban kuma majalisar ta amince da Barista Habib Dan-almajiri a matsayin shugaban hukumar zakka da hubusi ta Kano tare da membobinsa 14, sai kuma Sheikh Abbas Daneji a matsayin shugaban hukumar Shari’a, tare da Darakta Janar na hukumar Dr Sani Ashir.