Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da kudin hayar gidansa da ke Jihar Kaduna da ya bayar da shi yake cin abinci tare da rike kansa.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a Jihar Katsina a yayin wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar a yau Litinin.
Buhari ya bayyana cewa duk da shafe shekaru takwas da yayi akan karagar mulki, bai yi amfani da kujerar ba wajen azurta kansa ba.

Acewar Buhari Najeriya nada wuyar sha’ani musammaban ta fuskar jagoranci, wanda kuma ba a gane hakan sai lokacin da mutum ya tsici kanshi a ciki, inda ya kuma ce mafiya yawa daga cikin ‘yan Kasar ba su fahimci hakan ba.

Buharin ya kara da cewa a halin yanzu ya kara kyan ganu da kuma koshin lafiya, akan lokacin da ya na jagorancin Kasar.
Har ila yau Buhari ya bayyana cewa duk da shafe tsawon shekaru Takwas da yayi akan kujerar shugabancin Najeriya Amma gidaje Uku kadai ya mallaka, inda daya yake a mahaifarsa ta Daura, yayin da guda biyu kuma suke Jihar Kaduna.
Acewarsa a halin yanzu ya bayar da hayar gidansa daya da ke Jihar Kaduna, inda kuma yake samun kudin sayan abinci da kudin hayar gidan.