Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta yi holan wasu mutane da ta kama bisa aikata laifuka daban-daban a Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Salman Dogo Garba, ya ce daga cikin mutaen da aka kama ciki harda mutanen da suka yi garkuwa da wani tsohon jami’in gwamnati Mai suna Alhaji Atiku Ma’azu, inda wani mutum dan asalin karamar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa yayi garkuwa dashi tare da abokansa ‘yan Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa da yayi magana a madadin Kwamishinan, ya bayyana cewa jami’an sun kuma kama wasu ‘yan daba 16 a unguwar Kawo a Kano bayan sun fito akan titi su na kwace, tare da fasa motocin mutane uku, inda da kuma ta rundunar ‘yan sandan..

Sannan Kiyawa ya ce aikin rundunar ba iya kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya tsaya ba, harda karfafa alaka tsakaninsu al’umma don ganin an ci gaba da hada karfi da karfe, domin tabbatar da tsaro a Jihar.
Rundunar ta yi holan mutanen nen a Hekwatarta da ke Bampai a Kano a yau Laraba.
