Kungiyar matasan Jam’iyyar PDP ta ja kunnen gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad da ya kauracewa yin abubuwan da ka iya batawa jam’iyyar suna ko kuma ya fice daga cikinta.

Sannan kungiyar ta kuma bukaci da gwamna Bala da ya daina suka tare da cin mutuncin Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.

Shugaban kungiyar Comrd Isah Ibrahim, ya ce gwamnan Jihar ta Bauchi na yin hakan ne, domin yin amfani da jam’iyyarsa ta PDP domin ganin ya cimma burinsa.

Acewar Comrd Ibrahim Gwamna Bala na shukar gwamnatin shugaban Tinubu ba tare da wani dalili ba, wanda kuma ke zubar da kimar jam’iyyar ta PDP a fadin Kasar.

Shugaban ya ce ci gaba da sukar manufofin gwamnatin tarayya, musamman akan karin haraji, da gwamnan ke yi, duk da amincewa da kudurin da kungiyar gwamnoni ta Kasa ta yi, amma gwamna Bala na ci gaba da yin suka akan lamarin.

Har ila yau ta ce gwamnan nayin hakan ne don samun tikitin tsayawa takarar shugaban Kasa a shekarar 2027 a cikin jam’iyyar.

Kungiyar ta kuma bukaci da ya gwamnan yayi koyi da Wike domin gudanar da ayyuka masu amfani a Jiharsa.
Kungiyar ta kara da cewa matukar gwamna Bala ba zai daina zubar da martabar jam’iyyar ba, ya fice daga cikinta don bai’wa mambobinta da shugabanninta damar yin gyara a cikinta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: