Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake nada masu taimaka masa a bangarori daban-daban, tare da yiwa wasu sauye-sauye gurin aiki don kara tafiyar da gwamnatinsa yadda ya kamata.

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamna Abba ya amince da nadin hazikan mutanen ne domin kara bunkasa ayyukan gwamnatinsa.

Daga cikin wadanda gwamnan ya nada sun hada da Jamila Magaji Abdullahi wadda kwararriyace a harkokin kudi da haraji, da ta shafe sama da shekaru 16 ta na gudanar da aiki, kuma ita ce tsohuwar Daraktar Akanta a Ma’aikatar Kudi ta Jihar Kano.

Sannan gwamnan ya nada Muhammad Yahaya Liman wanda shima ya kwararren ma’aikacin banki ne kuma masanin harkokin kudi da ya shafe shekaru sama da 16 yana aiki.

Gwamnan ya kuma karawa Akibu Isa Murtala girma daga Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar zuwa Mai bada Shawara na Musamman kan Harkokin gudanarwa.

Gwamnan Abba ya kuma amincewa da sauyawa Injiniya Abubakar Sadiq mukami daga Mataimakin Darakta Janar na Kano Line zuwa RUWASA.

Sanarwar ta ce ta ce gwamnan yayi hakan ne domin hakan ya yi daidai da tsarinta na magance matsalolin muhalli da inganta rayuwar al’ummar karkara ta hanyar samar da ingantaccen ruwa da tsaftar muhalli.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an yi sabbabin nade-naden domin inganta harkar gudanar da gwamnatin jihar

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: