Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya amince da nadin mutane Takwas a matsayin masu ba shi shawara akan harkokin da suka shafi gwamnatinsa.

Mai magana da yawun gwamnan Muktar Gidado ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

Gidado ya ce gwamnan Bala ya nada munarnen bayan yin duba da tsakanin addinai wajen gudanar da nade-naden domin bai’wa kowa dama don ganin an dama dashi a harkokin gwamnatin.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce gwamnan na yin hakan ne don tabbatar da shugabanci nagari, hadin kai,da yin sauye-sauyen da za su taimaki rayuwar al’umma.

Daga cikin wadanda gwamnan ya nada sun hada da
Hon Sanusi Khalifa Toro a matsayin Mai bai’wa gwamna shawara akan harkokin ma’adanai.

Sai Hon Haladu Ayuba Dambam Mai bai’wa gwamna shawara akan inganta rayuwar al’umma.

Hon Jidauna Tula Bogoro kuwa mai bai ‘wa gwamna shawara akan harkokin shari’a, Hon Adamu Bello Giade mai bai’wa gwamna shawara akan bincike da masana’antu.

Sannan Alhaji Danladi Mohammed Danbaba Bauch mai bai’wa gwamna shawara kan harkokin jin kai, Hon Sani Mohammed Burra Ningi Mai bai’wa gwamna shawara akan harkokin majalisar jihar.

Sauran sun hada da Hon Yakub Ibrahim Hamza Darazo Mai bai’wa gwamna shawara akan harkokin ilimin gaba da sakandare, sai kuma Hon Shitu Zaki Zaki Mai bai’wa gwamna shawara akan harkokin siyasa.

Gidado ya ce an rantsar da mutanen ne a yau Talata a gidan gwamnatin Jihar, tare da wasu hadin uku da aka nada a baya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: