Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya bukaci al’ummar musulmin Najeriya da su fara duba watan Sha’aban daga gobe Laraba.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da wazirin Sokoto Farfrsa Sambo Junaidu ya fitar yau Talata.
Sanarwar ta buƙaci al’umma musulmi da su fara duba watan daga gobe Laraba yayin da watan Rajab ke cika kwana 29.

Sannan ta buƙaci alumma da su sanar da masu unguwanni ko dagatai ko hakimai mafi kusa don sanar da sarkin musulmi.

A cikin watan Sha’aban ne dai ake shiri don tunkarar watan Ramadan da ake azumtar dukkan kwanakinsa.