Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata jami’ar sojin ruwan Najeriya tare da wasu mutane biyu a wani hari da suka kai a daren jiya Juma’a a yankin Mamman Vatsa da ke kan hanyar Mpape a birnin tarayya Abuja.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Asabar.

Makama ya ce wasu majiyoyi sun shaida masa cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:45 na daren jiyan, a lokacin da maharan suka bude wuta a yankin daga bisa kuma suka gakuwa da mutanen.

Majiyoyin sun ce maharan su hudu da ke dauke da makamai, bayan zuwansu sun bude wuta a yankin, daga bisa kuma suka sace mutanen ukun.

Majiyoyin sun kara da cewa mutane da maharan suka sace sun hada da Laftanar Cynthia Ako da ta kasance jami’ar sojin ruwan Najeriya, sai Gold Alfred mazaunin yankin Bwari, sannan kuma wani mutum da ba a tantance sunansa ba.

Majiyoyin sun kuma cewa mutanen da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su na kan hanyarsu ne ta komawa gida a motarsu a bayan wata ziyara da suka kai ga wani dan uwansu mai suna Blessing Akor a Beggar Quarry Mpape.

Bayan faruwar lamari jami’an sojojin Najeriya da sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ‘ƴan sandan Abuja sun fara gudanar da bincike domin ganin sun kubtar da mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: