Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC Hukumar INEC ta ki amincewa da bukatar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, bisa rashin rubuta adireshinsu, lambobin wayarsu, ko kuma gmail din a cikin wasikar da suka aikewa da hukumar.

INEC ta ki amincewa da bukatar ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, mai dauke da sa hannun kwamishinan hukumar Sam Olumekun.
Sanarwar ta ce bayan mika bukatar yiwa Sanata Natasha kiranye da ‘yan Mazabarta su ka yi ga hukumar, sun gudanar da zama akan batun a taron da saba gudanarwa Mako-mako.

Hukumar ta kara da cewa hanyar dakatar da dan majalisa na cikin kundin tsarin mulkin Kasa na shekarar 1999, da dokar zaɓe ta shekarar 2022 da ta gabata da kuma ka’idojin hukumar na shekarar 2024.

Hukumar ta ce takardun korafe-korafen da ake kai’wa hukumar daga yankin na Kogi ta Tsakiya na hade da jakunkuna shida na takardu da aka bayyana na dauke da sa hannun sama da rabin masu zabe 474,554 ne daga rumfunan zaɓe 902 a yankunan rajista 57 da ke cikin kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori Magongo, da kuma Okehi da Okene.
Hukumar ta bayyana cewa wakilan masu shigar da korafi ba su cika dukka wata ka’idoji da ake bukata ba wajen yiwa dan Majalisar kiranye ba.
Sanarawar ta ce Adireshin da aka sanya a cikin takardar shi ne Okene a jihar Kogi, wanda ba tare da bayyana cikakken guri ba da za a iya tuntuɓarsu, sannan sun kuma bayar da lambar waya ta babban jagoran masu ƙorafi kadai maimakon lambobin dukan wakilan masu ƙorafi.
Hukumar ta ce da zarar an cika dukkan sharruddan Korafi tare da bin ka’idojin, hukumar za ta fara guanar da tantance sa hannun a rumfunan zaɓe ta hanyar tsari na buɗe ido da zababbun masu ƙorafi kadai za su shiga.
Acewar Hukumar za ta bi dukkan doka wajen tantance dukkan korafe-ƙorafen da ake aikawa hukumar.