Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa a yayin da shugaban Kasa Bola Tinubu ke cika shekaru 73 a duniya, zai a gudanar da addu’o’i na musamman a masallacin Kasa da ke Abuja a yau Juma’a.

Shugaba Tinubu zai cika shekaru 73 da haihuwa ne a gobe Asabar, 29 ga watan Maris 2025.
Mai magana da yawunsa kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.

Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su gudanar da addu’a domin samun shiriya daga Allah, hadin kai da kuma yiwa kasar Addu’o’in samun tabbaccen zaman lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Tinubu zai sadaukar da ranar zagayowar ranar haihuwarsa ta hanyar komawa ga Allah da yin addu’o’in samun zaman lafiya, cigaba da kuma wadata a Najeriya.
Onanuga ya ce shugaba Tinubu zai yi amfani da lokacin a yau din wajen mika godiyarsa ga Allah bisa tsawaita rayuwarsa da ya yi, tare da ba shi damar shugabantar Najeriya.
Sanarwar ta ce shugaban ya yi amanna da cewa yin addu’in bai daya na da matukar muhimmanci wajen jagorantar kasar zuwa ga cigaba da kuma samun daidaito.
Sannan ya mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya bisa goyon baya da kuma fatan alkhairi da ake yi masa, a lokacin da gwamnatinsa ke yin aiki tukuru don inganta tattalin arziki, karfafa tsaro, fadada samar da damarmaki ga ‘yan kasar, inda ya tabbatar da kudirinsa na karfafa dimokuradiyya, farfado da tattalin arziki, da kuma bunkasa hadin kan kasa.