Ministan harkokin matasa na Najeriya Comrd Ayodele Olawande ya bayyana cewa rashin lokaci ne ya hana shi shiga zanga-zangar da matasa ke yi a Kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a yau Litinin, yana mai cewa rashin wadataccen yayi masa katsalandan a shiga zanga-zangar da kungiyar Take It Back Movement ta fara a yau Litinin.
Ministan ya ce ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gurin taron shekara-shekara na masu yiwa kasa hidima NYSC a birnin tarayya Abuja.

Ministan ya yi kira ga matasan Kasar nan da su fito tar da bayyana abin da ke ransu, inda ya ja kunnensu da kaucewa lalata kayayyakin gwamnati da sunan yin zanga-zanga.

Olawande ya kara da cewa matasa na da ‘yancin bayyana ra’ayoyinsu, sai dai ya gargade su da gujewa tayar da rikici ko lalata gwamnati a lokacin zanga-zangar.
Acewarsa babu gwamnatin da za ta dakile mutane da yin zanga-zanga, sannan za a saurari dukkan korafe-korafen su, ya na mai cewa gwamnatin ta shirya tsaf domin jin karafe-korafen matasan Kasar tare da samar musu da mafita.
A yau Litinin ne dai kungiyar Take It Back Movement ta fara gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja da sauran sassan Kasar kan tsadar rayuwa, duk da gargadin da rundunar ‘yan sandan Kasar ta yi kan fitowa zanga-zangar.