Gwamnatin Jihar Sokoto ta gargadi mazauna Jihar da su kaucewa yin kalaman da ka iya kawo nakasu a kokarin da take yi na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar.

Mai bai’wa gwamna Jihar shawara na musamman kan sha’anin tsaro Kanal Ahmed Usman mai ritaya ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Gwamnatin ta Sokoto ta yi gargadin ne bayan bullar wasu kalamai da aka alakanta da wani mutum mai suna Basharu Altine Guyawa, na cewa gwamnatin Jihar ba ta sauke nauyin da ke kanta ba a sha’anin tsaron Jihar.

Acewar sanarwar irin wadannan kalamai ka iya ragewa al’ummar Jihar gwarin gwiwar da suke da ita akan gwamnati da jami’an tsaro a kokarin da suke yi na kawo karshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihar.

Kanal Ahmed ya bayana cewa sha’anin tsaro ba iya gwamnatin kadai ya shafa ba ya shafi kowa da kowa, inda ya ce gwamnati ita kadai ba za ta iya samar da tsaro ba, ba tare da goyan baya da hadin kan al’ummar ba.

Sanarwar ta bukaci mutanen Jihar da su kaucewa yada irin wadandan kalamai, da za su tayar da hankulan jama’a kuma siyasantar da lamarin tsaron.

Sanarwar ta kara da cewa da yin irin wadandan kalamai, ya kamata mutane su goyi bayan gwamnatin wajen samar da hanya mai dorewa ta kawo karshen matsalar rashin tsaron da Jihar ke fama dashi.

Kanal Ahmed ya ce Gwamnatin jihar hadin gwiwar dahukumomin tsaro na yin aiki ba dare ba rana domin ganin an wanzar da zaman lafiya a dukkan fadin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: